Masar: Kotun Koli ta haddasa cece-kuce

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga-zanga a Masar

Kotun koli a kasar Masar ta janyo kace-nace bayan ta yi shelar cewa, zaben majalisar dokokin da aka gudanar bara ya saba wa tsarin mulkin kasar tare da kiran a sake sabon zabe.

Kotun ta kuma soke wata dokar da ta so hana Ahmed Shafiq Prime Minista na karshe na gwamnatin Hosni Mubarak- tsayawa takara.

Masu fafutuka da manyan 'yan siyasar kasar sun zargi sojojin da kaddamar da juyin mulki.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta yi kiran a mika dukkan madafun iko ga zababbiyar gwamnatin democradiyya.