Ana ci gaba da tsare Farouk Lawan a Abuja

Hon Faruk Lawan Hakkin mallakar hoto google
Image caption Hon Faruk Lawan

Rundunar 'yan sanda a Najeriya na can na ci gaba da yin tambayoyi ga dan majalisar tarayyar nan da ya shugabanci kwamitin binciken yadda ake gudanar da harkar rarar kudaden cire tallafin man petur, watau Hon Farouk Lawan.

Rahotanni sun ce tun a daren jiya ne, rundunar ta ke tsare da dan majalisar a cigaba da bincke akan zargin karbar cin hancin kimanin dala dubu dari shida, domin ya wanke daya daga cikin Kamfanonin man da ake zargi da cin karen su ba babbaka a karkashin tallafin man.

Tun farko dai dan Majalisar ya musanta zargin, amma a wani taron manema labarai an ambato shi yana cewar ya karbi dala dubu dari biyar da nufin tona asirin wadanda ke kokarin ganin an wanke su daga binciken kwamitin.