Najeriya: majalisa za ta zauna yau

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Najeriya

A Nijeriya, yau ne Majalisar Wakilan kasar za ta yi wani zama na musammman don duba batun zargin karbar rashawa da ake yi wa kwamitin da majalisar ta kafa, wanda ya binciki yadda ake gudanar da harkar tallafin man fetur a kasar.

Ana zargin shugaban kwamitin da majalisar ta kafa don binciken yadda gwamnatin Nijeriyar ke gudanar da harkar tallafin man fetur wato, Hon. Faruk Lawan da karbar sama da dala dubu dari shida a matsayin toshiyar baki domin ya rufa wa wani Kamfanin mai asiri.

Shugaban daya daga cikin kamfanonin man Najeriya, Femi Otedola ne yayi zargin cewa, dan majalisa, Faruk Lawan ya karbi cin hanci da domin fitar da kamfaninsa daga cikin jerin kamafonin da kwamitin majalisar wakilan ya bincika.

Tuni hukumomin tsaro suka shiga cikin wannan batu, kuma 'yan Najeriya zasu sa ido domin ganin yadda majalisar za ta tunkari wannan zargi, wanda ba shi ne irinsa na farko ba.