An bada belin Hon Farouk Lawan

Faruk Lawan Hakkin mallakar hoto google
Image caption Faruk Lawan

A Najeriya hukumar 'yan sandan Kasar ta saki dan majalisar nan Hon Faruk Lawan wanda take rike da shi tun a ranar Alhamis, inda yake amsa tambayoyi.

Ana dai zargin Faruk Lawan ne da karbar cin hanci har dala dubu 620 daga hamshakin dan kasuwar nan Femi Otedola, domin ya cire sunan kamfaninsa daga cikin jerin kamfanonin da suka ci gajiyar kudaden tallafin mai ba tare da sun shigo da man Najeriya ba.

Hukumar 'yan sandan ta ce ta bada belin sa ne, bisa sharadin zai koma ofishinta ranar Litinin domin ci gaba da amsa tambayoyi.

A wani zaman gaggawa da majalisar wakilan Nijeriyar ta yi ranar Juma'a ta bada sanarwar dakatar da Faruk Lawan daga shugabancin kwamitin binciken rarar man petur da kuma shugabancin kwamitin Ilmi na majalisar.

Majalisar ta kuma kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa Hon Faruk Lawan din.

Wannan dai ba shi ne karon farko da zargin cin hanci ke dabaibaye irin kwamitocin binciken da majalisar ke kafawa ba.

Karin bayani