Bama-bamai sun tashi a coci-coci a Kadunan Najeriya

hari a Najeriya Hakkin mallakar hoto s
Image caption Harin kunar bakin-wake a Najeria

Wasu bama-bamai sun tashi a Zaria da kuma garin Kaduna a arewacin Najeriya inda jama'a da dama suka sami raunuka, wasu kuma suka rasa rayukan su.

Bama-baman sun tashi ne a unguwannin sabon gari da kuma wusasa a Zaria.

Hukumomi sun tabbatar da afkuwar al'amarin inda bayanai suka ce harin na kunar bakin wake ne.

Har yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda suka rasu ba.

Rahotanni na cewa an samu wani tashin bom din a garin Kaduna abin da ya haifar da hare-haren ramuwar gayya a yankin Kaduna ta kudu.

Hukumomi sun ce su na kan tattara kididdigar wadanda hare-haren suka rutsa da su.

Sakamakon halin da ake ciki gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar hana fita ta tsawon sao'i 24 a gaba dayan jihar har sai abin da hali ya yi.

Gwamnatin ta ce ta yi hakan ne domin hana bazuwar rikicin.

Karin bayani