'Yan adawan Syria sun ce ana ruwan bam a Homs

Wani sojan 'yan adawa a Syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani sojan 'yan adawa a Syria

Masu fafutuka a Syria sun ce ana ruwan bama bamai akan yankunan 'yan adawa a Homs kuma ana kara nuna fargaba akan cewa akwai daruruwan iyalan da lamarin ya rutsa da su.

Masu fafutukar sun ce a yau kawai, an kashe a kalla mutane arba'in a sassan kasar da dama.

Gwamnati kuma na cewa ta yi jana'izar sojojinta ashirin

Wannan karuwar tashin hankalin na zuwa a yayinda 'yan tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ke sa ido a Syriar suka kasance a masaukinsu bayan sun dakatar da aikinsu a kasar.

Sawsan Ghousha, wata mai magana ce da yawun tawagar majalisar dinkin duniyar a Syria, ta ce ba su so dakatar da aikin nasu ba. Ta ce a a kwanaki goma da suka wuce, sun lura cewa tashin hankali a kasar ya karu, kuma hakan ya sa ba sa iya sa ido sosai, ko su tabbatar da da abinda ke faruwa a kasar.

Ta kara da cewa ba sa kuma iya taimakawa, wajen ayyukan wanzar da zaman lafiya a kasar.