Ana tattaunawar kafa gwamnati a Girka

Antonio Samaras Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Antonio Samaras

Jagoran jam'iyyar masu matsakaicin ra'ayin rikau ta New Democracy ya ce kasar na bukatar a gaggauta kafa sabuwar gwamnatin hadin gwiwa.

Antonis Samaras na magana ne kwana guda bayan jam'iyyarsa ta samu nasara da kyar da jibin goshi, a zaben kasar, wanda ake yi ma kallon mai muhimmanci ga dorewar kasar cikin kasashe masu amfani da kudin Euro.

Mr Samaras ya yi alkawarin ci gaba da aiki da tsauraran sharuddan da kasashen duniya da suka baiwa kasar Girka tallafi suka gindaya ma ta, amma ya ce ya zama wajibi a aiwatar da wasu sauye sauye.

Yana tuntubar wasu jam'iyyun game da kafa gwamnatin gamin gambiza, amma jam'iyyar Syriza ,ta 'yan ra'ayin sauyi wadda ta zo ta biyu a zaben, ta ki shiga cikin shirin kafa gwamnatin saboda matukar adawar da take nunawa da matakan tsuke bakin aljihu.

Akwai alamun dake nuna cewa mai yuwa gwamnatin Jamus ta amince a rage tsaurin wasu daga cikin sharuddan na bai wa kasar ta Girka tallafi.

Ministan harkokin wajen Jamus yayi nuni da cewar mai yuwa a rage tsawon wa'adin da aka sa ma kasar ta Girka.

Karin bayani