An kashe mutane akalla hamsin a rikicin Kaduna - In ji Red Cross

Hakkin mallakar hoto AP

Kungiyar agaji ta Red Cross a Najeriya ta ce akalla mutane hamsin ne aka tabbatar an kashe, sannan wasu karin fiye da dari da talatin(130) suka samu raunuka, a sakamakon tashin hankalin da aka yi tsakanin Musulmi da Kirsta a Arewacin kasar a jiya, Lahadi.

Coci-coci guda uku ne dai aka kai ma harin kunar bakin wake a biranen Zaria da Kaduna, daga bisani kuma wasu matasa Kirista suka kai harin ramuwar gayya a kan Musulmi a garin na Kaduna.

Wannan al'amari ya sa hukumomin jihar ta Kaduna kafa dokar hana fita, tare da tura sojoji domin maido da doka da oda.

A yanzu an sassauta dokar hana fitar, inda zata fara aiki daga karfe shidda na safe zuwa shidda na yamma.

A wani sakon da ta aikewa da wasu kafofin yada labarai, Kungiyar nan ta Jama'atu Ahlus sunna lidda'awati wal jahad da aka fi sani da Boko Haram ta ce ita ke da alhakin hare haren bama baman da aka kaddamar jiya a Jahar Kaduna, tana mai cewar ramuwar gayya ce game da abin da ta kira "ta'asar da mabiya addinin Kirista suka shirya wa Musulmi a baya."

A dazu gwamnan jihar ta Kaduna, Mr Patrick Yakowa ya yi wata ganawa da manyan jami'an tsaro na jihar, a yunkurin lalubo hanyoyuin tabbatar da zaman lafiya.

Karin bayani