Sojoji sun ce za su mika mulki a Masar

Kidaya kuri'u a Masar Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Kidaya kuri'u a Masar

Majalisar mulkin sojan Masar ta ce za ta mika ragamar mulki ga sabon zababben shugaban kasa a wani biki da za a yi a karshen wannan watan. Har yanzu dai ba a bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a karshen makon da ya gabata ba.

Sai dai kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ta Muslim Brotherhood ta yi ikirarin cewa dan takararta, Mohammed Morsi ne, ya samu nasara a kan abokin takararsa, Ahmed Shafiq, wanda tsohon Janar ne na rundinar mayakan saman kasar, kuma tsohon praminista karkashin gwamnatin Hosni Mubarak.

Mr Shafiq din dai ya yi watsi da ikirarin na kungiyar ta 'Yan Uwa Musulmi, yana mai cewa yayi wuri, wani yayi ikirarin samun nasara.

A halin da ake ciki kuma, daruruwan magoya bayan Mohammed Morsi suna hallara a dandalin Tahrir, domin shagulgulan murnar nasarar da suka ce ya samu a zaben.

Yayinda aka kusa kammala kidaya kuri'un, alamu na nuna cewa Muhammad Mursi an shirin lashe zaben da dan karamin rinjaye.

Ministan tsaron kasar Isra'ila Ehud Barak ya ce akwai bukatar duk wanda ya samu galaba a zaben ya tabbatar da harkokin tsaron Gabas ta Tsakiya.

Karin bayani