Villas-Boas na takarar mukamin kocin Spurs

Hakkin mallakar hoto AP

Kungiyar Tottenham Hotspur ta gana da wakillan tsohon kocin Chelsea Andre Villas-Boas, a kokarinta na nada sabon koci a kungiyar.

Kungiyar ta tunkari wakilan koci ne mai shekarun haihuwa 34, su ji ko yana da sha'awar jagorantar kungiyar, kuma akwai yiwuwar a gana da shi a makon da muke ciki.

Shugaban kungiyar Daniel Levy ne da kansa zai jagoranci tantancewar daukar sabon kocin.

Kocin Faransa Laurent Blanc na cikin wadanda ake zawarcinsa domin jagorantar kungiyar.

Tottenham dai ta sallami kocinta na da Harry Redknapp a ranar Laraban da ta gabata, bayan kusan shekaru hudu yana jagorancin kungiyar.