Bama- bamai sun tashi a Damaturu

An kai hari Damaturu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kai hari Damaturu

Rahotanni daga Damaturu babban birnin jihar Yobe dake Arewacin Najeriya, sun ce mazauna unguwanni da dama ne suka tsere daga gidajen su, yayin da wasu karin suka kauracewa unguwannin su domin samun mafaka.

Wannan dai ya biyo bayan tashin bama bamai da karar bindigogin da aka rika ji ne ba kakkautawa a yammacin yau.

Rundunar Hadin Gwiwar Samar da tsaro a jihar Yoben ta tabbatar da abkuwar lamarin, sai dai ba ta bayyana adadin asarar rayuka da jikkata da aka samu ba a sakamakon wannan hari.

Harin na Yoben dai na zuwa ne kwana daya bayan wasu hare haran kunar bakin wake da aka kai kansu coci-coci uku a garin Kaduna da kuma Zaria.

Hare haran da kungiyar Ahlisunna lidda'awati wal jihad da ake kira Boko Haram suka yi ikirarin kaiwa.

Karin bayani