Za a hukunta sojojin da suka kona Alkur'ani

Hakkin mallakar hoto
Image caption Sojojin NATO da ke aiki a Afghanistan

Jami'an Amurka sun ce wani binciken soji game da kona Alkur'ani a wani sansani da ke Afghanistan ya bayar da shawarar ladabtar da dakaru bakwai.

Jami'an da ba su amince a bayyana sunansu ba sun ce an gabatar da rahoton binciken ga ma'aikatar tsaron Amurka inda yanzu take nazari a kansa.

Kona Alkur'anan a watan Fabrairu ta jawo zanga-zanga da hare-hare a kan dakarun kungiyar tsaro ta NATO a kasar Afghanistan.

Hukumomi a Afghanistan sun sha zargin sojojin kasashen waje da ke aiki a kasar da musgunawa 'yan kasar.

Karin bayani