Mubarak na cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hosni Mubarak

Har ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa daga hukumomin kasar Masar dangane da halin da tsohon shugaba Mubarak wanda aka yankewa hukumcin daurin rai da rai yake ciki.

Wasu daga cikin magoya bayansa da suka taru a harabar asibitin sun ce ba zasu manta da irin tsaron da ya kawowa kasar ba.

Da fari dai, kamfanin dillancin labaran kasar ya ruwaito cewa likitoci sun ce Mista Mubarak, da aka yankewa hukuncin daurin rai-da-rai na gargarar mutuwa.

Daga bisani rahotannin sun ruwaito jami'an tsaro da na asibiti na cewa dogon suma ya yi kuma an dora shi a kan na'urar da ke taimakawa mutum yin numfashi.

Labarin mutuwar Hosni Mubarak bai dada masu zanga-zanga da kasa ba, da yawansu ma ba su amince da rahotannin ba inda suke zargin an fake da rashin lafiyarsa ne an fitar da shi daga jarun.

Ana kambama yanayin rashin lafiyarsa

Tun bayan da aka tunbuke Hosni Mubarak daga karagar mulki an yi ta samun rahotanni game da tabarbarewar lafiyarsa, amma a duk lokacin da rahotannin suka bayyana 'yan kasar kan yi dari-dari kafin amincewa da su.

Sai dai a daren ranar Talata gidan talabijin da kamfanin dillancin labarai na kasar sun ce tsohon shugaban na gargarar mutuwa.

A cewarsu, zuciyarsa ta daina aiki a yayin da aka fitar da shi daga kurkukun da yake ciki zuwa wani asibitin soji da ke wajen kurkukun.

Sun kara da cewa duk wani yunkuri da aka yi na fardado da shi daga dogon suman da ya ke ciki ya ci tura.

Sai dai jami'an gwamnati sun ce an sanyawa tsohon shugaban na'urar da ke taimaka masa yin numfashi ne ba wai mutuwa ya yi ba.

Wani Janar a Majalisar Sojin da ke mulkin kasar ya ce maganganun da ake yi cewa Mista Mubarak na halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai shirme ne kawai.

A watanni da dama da suka gabata dai, 'yan kasar Masar na ganin iyalan Mista Mubarak na kambama halin rashin lafiyar da yake ciki ne, ko dai domin ba sa so a yi masa shari'a ko kuma, a halin da ake ciki, domin a fitar da shi daga kurkuku zuwa wani waje da zai fi samun sa'ida.

Gabanin a yanke wa Mista Mubarak hukunci, lauyansa ya ce tsohon shugaban bai san a halin da yake ciki ba amma kwatsam sai aka ga tsohon shugaban ya bayyana a cikin hayyacinsa.

'Yan kasar dai na ganin batun rashin lafiyar ta sa wata dabara ce da mahukunta ke son yi don karkatar da hankalin jama'a daga sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar.

Karin bayani