Ana taro a kan inganta muhalli

Image caption Birnin Rio De Janeiro

Wakilan da ke halartar taron kare muhalli a Brazil mai nazari a kan shekaru a shirin bayan taron da aka gudanar a Rio a shekarar 1992 sun amince da daftarin manufofin dora tattalin arzikin duniya a kan tafarki mai dorewa.

Sai dai an zargi daftarin, wanda shugabannin duniya za su sanyawa hannu ranar Juma'a, da rauni saboda gaza tantance abubuwan da ake son a cimma da kuma lokutan da za a cimmasu.

Daftarin dai ya cire wani sakin layi da ya bukaci gwamnatoci su janye tallafin da suke bayarwa a kan makamashin da ake hakowa a kasa.

Haka kuma ya dage daukar mataki a kan kula da tekunan duniya zuwa shekaru uku masu zuwa.

Karin bayani