G20 ta nemi kasashen Turai su kyautata tattalin arzikinsu

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Shugabannin kungiyar kasashen G20

Shugabannin kasashe ashirin da suka fi arziki a duniya sun bukaci kasashen Turai su dauki duk matakan da za su iya wajen warware rikicin bashin kasashen da ke amfani da kudin Euro.

Wani daftarin sanarwar bayan taro na shugabannin, wadanda ke taro a Mexico ya bayyana cewa a shirye suke su dauki matakan da suka dace don tabbatar da bunkasar tattalin arzikin duniya.

Ya kara da cewa za su karfafa gwiwar masu zuba jari domin su sanya kudinsu a fannoni daban-daban na tattalin arziki.

Shugabannin na nuna damuwa ne kan yadda mummunan yanayin tattalin arzikin da Turai ke ciki ke dada yin tasiri a kan tattalin arzikin kasashen yammacin duniya.

Wannan batun dai shi ya mamaye tattaunawa a taron inda zargin da wani dan jarida ya yi cewa sakacin shugabannin Turai ne ke ta'azzara al'amarin ya jawo kakkausan martani daga shugaban Hukumar Tarayyar Turai, Jose Manuel Barroso.

Ya ce:''Wannan matsalar fa ba daga Turai ta taso ba, daga Arewacin Amurka ta yi tushe kuma yawancin bankunanmu sun shiga tsaka-mai-wuya ne sanadiyyar badakalar da aka tafka a Amurka''.

Karin bayani