An nada sabon piraminista a kasar Girka

Hakkin mallakar hoto greece

An rantsar da sabon piraminista a kasar Girka don ya jagoranci gwamnatin hadin-gwiwa a kasar.

Antonis Samaras, shugaban jam'iyyar New Democracy, wadda ta ta yi nasara a zaben da aka yi ranar Lahadi da kan-kanen rinjaye, shine ya zama sabon piraministan.

Jam'iyyun da suka shiga cikin gwamnatin hadin gwiwar dai sun hada harda jam'iyyar 'yan gurguzu ta PASOK da kuma wata karamar jam'iyya da ake kira Demoratic Left.

Ana sa ran cewa sabuwar gwamantin za ta yi kokarin shawo kan masu bada lamuni na duniya da su saukaka sharuddan da aka shimfidawa kasar na samun basussukan ceto ta daga matsalar tattalin arziki.

Ana ganin cewa wannan batun din ne zai taimaka wajen ci gaba da kasancewar kasar cikin kungiyar kasashen dake amfani da kudin Euro.

Jagoran jam'iyyar 'yan gurguzu, Evangelos Venizelos, ya ce wannan shine babban yaki na farko dake gabansu.

Tunda farko dai Mista Venizelos ya ce amince da ya marawa Mista Samaras baya domin kafa gwamnatin hadin gwiwar.

Karin bayani