Sabon rikici ya sake barkewa a wasu unguwannin Kaduna

Wasu gidaje da aka kona a Kaduna Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu gidaje da aka kona a Kaduna

Rahotanni daga Najeria na cewa wani sabon rikici ya barke yau a wasu unguwanni dake cikin garin Kaduna, tsakanin matasan musulmai da na kirista.

Hakan dai ya faru ne dukuwa da dokar hana fita ta sa'o'i 24n da aka sa a duk fadin jahar tashin hankalin na baya-bayan nan ya faru ne a unguwar Kujama inda aka yi kone-kone, sakamakon wata

rigima da ta taso tsakanin matasan, bayan da aka yi zargin cewa wasu matasa kirista sun ki biyan wata yarinya musulma mai saida kwai kudinta.

Tun farko a yau kuma, an yi dauki ba dadi tsaknin matasan musulmai da kirista a unguwanni hudu na Kadunan da suka hada da Badarawa da Marayi .

Ana dai fama da rikice rikice ne tun bayan harin bom din da aka kai wasu chochi uku a kaduna da zaria da kuma hare haren ramuwar gayyar da suka biyo baya.

Domin kawo karshen wannan matsala ne dai shugaban 'yan sanda na kasar da shugaban rundunonin sojin najeriyar suka je kaduna don lalumo bakin zaren.

Har yanzu dai babu bayani game da ainihnin yawan wadanda suka rasa rayikansu ko kuma su jikkata a sakamakon wannan sabon rikici.

Karin bayani