Paparoma ya yi kiran samar da zaman lafiya a Nigeria

Rikicin Kaduna Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rikicin Kaduna

Paparoma Benedict ya yi kiran da a kawo karshen abinda ya kira hare haren ta'addanci da ake kaiwa kan mabiya addinin kirista a Najeriya nan take, ya kuma yi kira ga duka bangarorin da su guji yin ramuwar gayya.

Kiran na Paparoma dai ya biyo bayan rikicin da ya barke ne a jahar Kaduna dake arewacin kasar, inda kungiyar masu kaifin kishin Islama ta Boko Haram ta kai hare haran bama- bamai kan wasu mujami'u a jahar

Lamarin ya haddasa tashin hankali tsakanin Musulmai da mabiya addinin kirista.

Paparoma Benedict na 16 yayi wannan kiran ne a karshen wani jawabi da yake yi mako-mako gaban manyan jam'ian cocin sa a fadar sa dake Vatican yau laraba.

Paparoman ya ce yana biye da abubuwan da ke faruwa a Najeriyar cike da matukar damuwa ganin yadda wadanda ya kira y'an ta'adda ke kai hare hare kan al'ummar kiristoci.

Karuwar rikici a Najeriyar ya shigar da fargabar barkewar yakin basasar addini a zukatan jama'ar kasar, wadda ta dauki watanni tana fama da hare-hare kan Majami'u, da gine-ginen gwamnati da wasu wuraren da kungiyar wadda ake kira boko haram ke daukar alhakin kaiwa.

Karin bayani