An bude babban taron duniya kan cigaba mai dorewa a birnin Rio de Janeiro

Ban Ki-moon Hakkin mallakar hoto UN
Image caption Ban Ki-moon

Babban sakatar janar na Majalisar dinkin duniya, Ban Ki- moon ya yi gargadin cewa lokaci na kurewa a yunkurin da ake na tunkarar matsalolin da suka shafi muhalli.

Mr Ban ya yi wannan furucin ne a lokacin da yake jawabi wajen bude babban taron kasashen duniya kan batun ci gaba mai dorewa da ake a birnin Rio de Janeiro na Brazil.

Ya kuma yi kira ga wakilan kasashen duniya da su yi rika aiwatar da abinda suka furta wajen kawo ci gaba mai dorewa.

Ya ce dole ne shugabannin kasashe su aike da sakonni cewa sun yi amannar kawo sauyi game da makomar kasashen nasu, makomar da za ta fitar da jama'a daga kangin talauci da sauransu.

Karin bayani