An zargi Pakistan da musgunawa Amurkawa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Barack Obama

Wani rahoton ma'aikatar hulda da kasashen waje ta Amurka ya ce musgunawar da mahukuntan Pakistan ke yi wa jami'an diplomasiyyar Amurka ya yi matukar karuwa har yana barazana ga aiwatar da aikinsu.

Rahoton ya ce musgunawar ta kara tsananta ne bayanda Amurka ta kai hari kan gidan da Osama bin Laden ya zauna da kuma wani harin dakarun NATO da ya kashe sojin Pakistan ashirin da hudu a bara.

A cewar rahoton, Pakistan na jan kafa wurin baiwa jami'an Amurka visa, suna kuma hana aiyukan gine-gine da tallafi, tare da sa ido kan ma'aikata da 'yan kwangila na ofishin jakadancin Amurka.

Rahoton dai ya ce ya zama wajibi gwamnatin Amurka ta tattauna da ta Pakistan don kawo karshe lamarin.

Karin bayani