Bankin Amurka ya rage hasashen tattalin arziki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Barack Obama

Babban bankin Amurka ya rage hasashensa dangane da farfadowar tattalin arzikin kasar cikin wannan shekara, saboda an samu tafiyar hawainiya a farfadowar da tattalin arzikin ke yi.

Babban bankin yace, ya rage hasashen farfadowar tattalin arzikin ne daga kashi biyu da digo tara zuwa kashi biyu da digo hudu saboda tattalin arzikin kasar na fuskantar barazana daga tasirin matsalar bashi da kasashen dake amfani da kudin Euro ke fuskanta.

Shugaban Hukumar kula da lalitar gwamnatin kasar Ben Bernanke, ya ce bankin a shirye yake yayi duk abinda zai yi da ya zama wajibi don tallafawa tattalin arzikin.

Masu saka hannu jari dai na fatan Hukumar zata samarda matakai masu karfi.

Sai dai wannan tafiyar hawainiyar da bunkasar tattalin arzikin Amurkan keyi a wannan lokaci wani labari ne mara dadi ga Shugaban Kasar Barack Obama a shekarar da zai fuskanci kalubalen zabe.

Karin bayani