China za ta binciki dalilin mutuwar dan Najeriya

Firimiyan China Wen Jiabao Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Firimiyan China Wen Jiabao

Kasar Sin ta ce za ta bincika batun mutuwar da wani dan Najeriya ya yi a lokacin da 'yan sandanta suke tsare da shi a garin Guangzhou da ke kudancin kasar.

Chinan ta bayyana hakan ne, bayan 'yan Afrika da dama sun gudanar da zanga-zanga domin nuna alhininsu ga kisan dan Najeriyan, kuma ofishin jakadancin Najeriya ya yi kiran da a bincika mutuwar dan kasar ta ta.

Dan Najeriyar mai shekaru ashirin da takwas wanda kafofin yada labarai suka bayyana sunansa Elebachi Celestine, 'yan sanda sun tsare shi ne bayan ya yi fada da wani dan tasi a kan kudin da dan tasin ya cajesi ranar litinin da ta wuce.

Bayan da 'yan sandan su ka tafi da shi ofishinsu ne ya rasu a can wanda hakan ya sa wasu 'yan kasashen Afrika kusan su 100 su ka yi zanga zanga a washegari.

Wasu bayanai da aka rubuta a shafukan internet sun yi zargin cewa wasu tarin 'yan kallo ne 'yan China da suka taru lokacin da dan Najeriyar ke rigima da dan tasin su ka yi ma sa duka.

Kakakin ma'aikatar harkokin kasashen waje na China, Hong Lei, ya ce za su gudanar da bincike a kan lamarin kamar yadda doka ta tanada ba tare da wani bata lokaci ba kuma su baiwa hukumomin Najeriya bayani.

Tuni dai hukumomin Guangdong ,lardin da birnin da abin ya faru su ka shedawa ofishin jakadancin Najeriya game da mutuwar dan kasar ta ta.

Sai dai ba su bada karin bayani dalla-dalla game da sanadin mutuwar mutumin ba.

Wata jaridar kasar ta Sin ta ruwaito kakakin ofishin jakadancin Najeriya, Ademola Oladele, na cewa su na fatan za a basu rahoto mai zaman kansa na musabbabin mutuwar dan Najeriyar.

Ta re da fatanbn za a yi adalci a kan lamarin yadda ya kamata don kada lamarin ya shafi kyakkyawar alakar da ke tsakanin Najeriaya da Sin din.

Karin bayani