Wasu kungiyoyi a Nijar sun yi gargadi kan rikicin Mali

Wasu 'yan tawayen Arewacin Mali Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu 'yan tawayen Arewacin Mali

A jamhuriyar Nijar, kawancan wasu kungiyoyin farar hula na kasar sun bayyana matsayinsu a kan rikiciin kasar Mali da ma yadda kungiyar ECOWAS ko CEDEAO da gwamnatin Nijar ke tunkarar matsalar a kokarinsu na shawo kanta.

Kawancen kungiyoyin dai na ganin zai fi kyau ECOWAS ta fifita neman hanyar sulhu maimakon amfani da karfin soja a kasar ta Mali, saboda a cewarsu yin hakan zai iya jawo bazuwar yakin a sauran sassan yankin sahel.

Haka nan kuma kungiyoyin sun yi kira ga shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar da ya rika sara yana dubin bakin gatari dangane da rikicin na kasar ta Mali.

Karin bayani