An kusa kammala shariar Breivik

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Breivik

A yau ne za'a kare shari'a mafi girma a tarihin kasar Norway inda lauyoyin da ke kare Anders Behring Breivik za su kammala jawabansu.

Breivik dai ya yi ikirarin kashe mutane saba'in da bakwai, mafi yawansu matasa, a hare-hare guda biyu da ya kai a bara.

Masu shigar da kara dai na neman kotu ta bayyana shi a matsayin mai tabin hankali; ta kuma yanke masa hukuncin zuwa asibitin mahaukata, sai dai ya musanta wannan zargi inda lauyoyinsa ke bukatar a tura shi gidan kurkuku.

Nan gaba ne kuma ake sa ran kotun za ta bayyana hukuncin da ta yanke.

Karin bayani