Kotun Pakistan ta ce a kamo Firai minista mai jiran gado

Yousuf Raza Gilani Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsohon fira ministan Pakistan Yousuf Raza Gilani

Wata kotu a Pakistan ta bada sammacin kama Makhdoom Shaha-buddin, mutumin da jam'iyyar dake mulki a kasar ta PPP ta zaba domin a bashi mukamin Fira minista.

A ranar talata ce kotun kolin kasar ta haramtawa tsohon Fira minista, Yusuf Raza Gilani rike mukamin, a wani mataki da ba safai kotun kan dauka ba.

Ranar Juma'a ce kuma majalisar dokokin kasar za ta zabi wanda zai cike gurbin Fira ministan.

Shi dai Shabuddin ya ce laifinsa kawai shi ne yana rike da mukammin ministan lafiya ne lokacin da abin kunyar da aka yiwa lakabi da Chemical Quota Case ya bayyana wanda a dalilin hakan ne kotun ta ke nemansa.

Haka ma jami'an da ke bincike kan safarar magunguna ba bisa ka'ida ba sun zargi har da dan fira ministan da aka tumbuke watau Ali Musa Gilani da hannu cikin wannan lamari.

Koda yake kamar Shahabuddin, shi ma Ali Gilanin ya musanta zargin.

Har yanzu dai ba ta fito fili ba ko bayar da umarnin kama Makhdoom Shahhbuddin zai shafi mika sunansa da gwamnati tayi a zaman wanda majalisar dokokin kasar zata nada a zaman fira minista.

Amma a halin da ake cikin Jamiyyar sa ta PPP bayar da sunan wani mutun na biyu shima a zaman wanda za'a nadan a mukamin na Fira Minista.

Wanda aka bayar da sunan nasa dai wani tsohon Ministan watsa labaran kasar ne mai suna Kamaruzzaman Kaira.

Kowanne ne dai ya zamo Fira ministan kasar zai samu al'ummar kasar a fusace saboda jerin matsalolin da kasar ke fuskanta a halin yanzu da kuma kalubalen yadda zai yi tafiya tare da alkalin Kotun kolin kasar wanda ke alfahari da kansa a zaman wanda ya kara da 'yan siyasa mafiya karfi a kasar kuma ya sha.