Cyprus ta bukaci tallafin kudi daga Turai

Shugaban Cyprus Dimitiris Christofias da Kwamishinan Fadada Tarayyar Turai Stefan Fule Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Cyprus Dimitiris Christofias (a dama) da Kwamishinan Fadada Tarayyar Turai Stefan Fule

Kasar Cyprus ta bukaci kungiyar Tarrayar Turai ta samar mata da kudi don ceto tattalin arzikinta.

Gwamnatin kasar ta Cyprus ta ce bankunanta na fama da matsaloli saboda dinbim basussukan da suke bi a kasar Girka.

Rahotanni sun nuna cewa banki na biyu mafi girma a Cyprus na bukatar tallafin gaggawa.

Wani masanin tattalin arziki, Justin Urquhart, ya bayyana cewa:

“Ba na tunani za a ba su bashin ba tare da wadansu sharudda ba, saboda alakarsu da Girka, kuma ba a so a fara nuna bambamci a cikin lamarin”.

Kasar ta Cyprus dai ta kasance kasa ta biyar dake amfani da kudin Euro da ta bukaci tallafi don ceto tattalin arzikinta, bayan kasashen Jamhuriyar Ireland, da Portugal da Girka da kuma Spain.

Karin bayani