Ko wanene sabon shugaban Masar Muhammad Mursi?

Muhammad Mursi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zababben Shugaban Masar, Muhammad Mursi

Zababben Shugaban Masar na farko da aka zaba bisa tsarin dimokuradiyya, Muhammad Mursi, ya fara aikin nada tawagar da za ta jagoranci gwamnatinsa.

Malam Mursi dai ya shiga ofishin da a da tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak ya zauna.

Wani na hannun damansa ya ce ya fara tattaunawa da kuma yin tuntuba game da kafa wata sabuwar gwamnati.

A jiya dai ya bukaci hadin kan kasa, yana cewa juyin juya halin da ya kawar da Shugaba Mubarak zai ci gaba har sai ya cimma burinsa.

To abin tambaya a nan shi ne ko wanene Muhammad Mursi?

Muhammad Mursi dai dan asalin wani kauye ne da ke lardin Sharkiya a wani wuri da Kogin Nilu ya hadu da Tekun Maliya.

Ya yi karantun injiniya a Jami'ar Alkahira a shekarun 1970 kafin daga bisani ya je Amurka inda har ya kammala digiri na uku.

Bayan da ya koma Masar ya kasance shugaban Sashen Nazarin Aikin Injiniya a Jami'ar Zagazig; a lokaci guda kuma ya rike mukamai a kungiyar 'Yan Uwa Musulmi, wato Muslim Brotherhood.

Malam Mursi dai ya kasance dan majalisar dokoki na independa a bangaren 'Yan Uwa Musulmi daga shekarar 2000 zuwa 2005.

Lokacin da ya ke rike da mukamin dan majalisa an yaba masa saboda kaifin bakinsa, abin da ya sa kuma daga baya aka zabe shi a matsayin mai magana da yawun 'Yan Uwa Musulmi.

Bayan tayar da kayar bayan da aka yi a kasar ya tilastawa Hosni Mubarak sauka daga kan mulki, Muhammad Mursi ya zamo shugaban jam'iyyar Freedom and Justice Party.

Malam Mursi dai ya mika takardunsa na neman tsayawa takarar shugabancin kasar kwana daya bayan da ta bayyana cewa za a iya hana wanda jam'iyyar ta Freedom and Justice Party ta tsayar takarar, hamshakin dan kasuwa kuma mataimakin shugabanta, Khairat Al-Shatir, daga tsayawa takara.

Kuma bayan da aka haramtawa Al-Shatir da wadansu 'yan takarar tsayawa a hukumance, sai kungiyar ta 'Yan Uwa Musulmi ta mayar da goyon bayanta a gare shi.

Image caption Magoya bayan Muhammad Mursi bayan bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara

Kwararren injiyan mai shekaru sittin da haihuwa dai ya samu kashi ashirin da hudu cikin dari na kuri'un da aka jefa a zagayen farko na zaben shugaban kasar a watan Mayu, wato ya zo na biyu bayan Ahmed Shafik, tsohon hafsan sojan sama wanda ya yi aiki a matsayin firayim minista na gajeren lokaci a gwamnatin Hosni Mubarak.

Amma da aka yi zagaye na biyu na zaben sai ya samu kashi hamsin da biyu cikin dari na kuriun da aka jefa.

Yanzu dai Muhammad Mursi ya fara kokarin kawar da tunanin da ake yi cewa shi mai zafin kishin addini ne kuma zai sanya kungiyarsa ta mamaye fagen siyasar kasar.

Ya ce ba dole ba ne ya zabo firayim minista daga jam'iyyarsa ta FJP wadda ke da rinjaye a majalisa, kuma zai nada wani daga cikin kibdawa Kiristoci ya zama mai ba shi shawara; mai yiwuwa ma ya zama mataimakinsa.

Karin bayani