Mutane sun dan samu fita a Kadunan Najeriya

Barnar rikicin Kaduna Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Barnar da rikicin Kaduna ya haifar

Jama'a sun samu damar fita bayan da aka sassauta dokar hana fita a birnin Kaduna da ke arewacin Najeriya, inda al'ummar Musulmi suka fita domin yin sallar Juma'a.

Ko da ya ke an sassauta dokar a yau Juma'a, gobe za ta ci gaba da aiki ba dare ba rana.

Haka kuma a ranar Lahadi za a sake sassautawa domin baiwa Kiristoci damar zuwa wuraren ibada.

A sakamakon sassauta dokar dai mutane da dama sun fita domin biyan wadansu daga cikin bukatunsu.

A halin da ake ciki kuma, yayinda ake kokarin shawo kan matsalar tashe-tashen hankulan da ke aukuwa a arewacin kasar ta Najeriya, gwamnoni da jami'an tsaro suna ta bin matakai daban-daban a yankin kudu maso gabashinta, don magance kai hare-hare irin na ramuwar gayya a kan 'yan arewa mazauna yankin.

Har ma gwamnan Jihar Anambra, Mista Peter Obi, ya yi wani taro na musamman da sarakunan gargajiya da sauran shugabannin al'umma, don jaddada bukatar zaman lafiya.

Gwamnan ya yi kira ga kowa da kowa ya kwantar da hankali, kuma a guji kai hare-haren ramuwar gayya ko tunanin haka a kan 'yan arewa.

Ya kuma bayar da tabbaci cewa (a matsayinsa na shugaban taron gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya), yana tuntubar takwarorinsa na arewa da ma sauran sassan kasar, don ganin an sami zaman lafiya.

A duk lokacin da aka samu wata tashin-tashina ko hatsaniya a arewacin kasar dai, al'amarin ya kan tayar da kwannafin ramuwar gayya a yankin kudu maso gabas saboda yadda rikice-rikicen na arewa kan shafi al'ummar yankin da ke zaune a arewar.

Karin bayani