Mutane miliyan daya na bukatar taimako a Syria

Kofi Annan da Manjo Janar Rebert Mood Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wakilin Majalisar Dinkin Duniya ga Syria, Kofi Annan da Manjo Janar Rebert Mood

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane miliyan daya da dubu dari biyar na bukatar taimako a Syria - adadin da ya haura kiyasin da aka yi a baya da kusan mutane dubu dari biyar.

Ofishin Majalisar ta Dinkin Duniya mai kula da shirin tallafawa jama'a ya ce yawan mutanen da ke tserewa daga gidajensu na karuwa saboda fadan da ake yi; kuma rikicin na kawo cikas ga kokarin raba kayan agaji.

An dakatar da wata yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Majalisar da gwamnatin Syria a kan bayar da taimako saboda matsalar tsaro.

A halin da ake ciki dai an gano gawarwakin wadansu mutane ashirin da shida a garin Aleppo da ke arewacin kasar ta Syria.

Kungiyar 'yan adawa ta Syrian Observatory for Human Rights ta ce ta yi amanna cewa sojojin sa-kai ne na Shabbiha masu goyon bayan gwamnati aka kashe a matsayin ramuwar gayya, bayan gwamnatin ta yi makwanni tana kai hare-hare a yankin.

Sai dai gwamnatin kasar ta Syria ta ce gawarwakin fararen hula ne wadanda mutanen da ta kira 'yan ta'adda masu yaki da makamai suka kashe.