Za mu dau mataki kan harbo jirginmu —Turkiyya

Samfurin jirgin Turkiyya da Syria ta harbo Hakkin mallakar hoto AIRTEAMIMAGES
Image caption Samfurin jirgin Turkiyya da Syria ta harbo

Mataimakin Firayim Ministan Turkiyya, Bulent Arinc, ya ce harbo jirgin saman yakin kasarsa da Syria ta yi abu ne da ba za a bari ya wuce ba tare da daukar mataki ba.

A cewarsa, Turkiyya za ta kare kanta a bisa tanade-tanaden dokokin kasa da kasa.

Mista Arinc ya kuma tabbatar da cewa dakarun gwamnatin Syria sun harbi wani jirgin saman ceto na Turkiyya wanda ya je duba baraguzan jirgin saman yakin da aka harbo a makon da ya gabata; sai dai jirgin na biyu da aka harba bai fado kasa ba.

Shi kuma kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Turkiyya, Selcuk Unal, ya musanta cewa matukin jirgin saman da aka harbo ya aikata ba dai dai ba.

“Jirgin ba ya dauke da makamai kuma yana kan hanyarsa ta zuwa wadansu gwaje-gwaje ne a kan wadansu sababbin na'u'rorin da aka sanya a wani filin jirgin sama”, in ji Mista Unal.

Karin bayani