Rikicin Kaduna ya hana tafiya zuwa Abuja

Abin da ya rikicin Kaduna ya haddasa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abin da ya rikicin Kaduna ya haddasa

A Najeriya, tashe-tashen hankulan da suka faru a Kaduna da kuma dokar hana zirga-zirgar da aka sa a jihar sun tilastawa daruruwan matafiyan da ke bi ta jihar zuwa Abuja, babban birnin kasar, fasa tafiye-tafiyensu.

Wadansunsu kuma kan bi wadansu hanyoyin na daban, wadanda kan sa su dauki dogon lokaci kafin kaiwa inda suka nufa.

Wani mai harkar zirga-zirga tsakanin Kano da Abuja, Isa Abubakar Imam (wanda aka fi sani da Alhaji Babba) ya shaidawa wakilin BBC a Kano, Yusuf Ibrahim Yakasai, cewa fasinjoji sun zama kamar an yi ruwa an dauke.

“Akwai hanyoyin da za a yi zagaye don kaucewa bi ta Kaduna, amma al’amari ne na kudi, domin in ka yi wannan zagayen zuwa Abuja [motarka] za [ta] sha tanki biyu na man fetur. [Saboda haka] sai ko wanne fasinja ya biyanmu [Naira] dubu hudu da dari biyar muke zagawa”.

Wadanda ke da hali kuwa na hawa jiragen sama ne domin tafiye-tafiyen nasu.

Wannan al’amari dai ya sa tikitin jirgin sama ya yi wahalar samu matuka, kamar yadda wani matafiyi mai suna Alhaji Ibrahim Abbas ke cewa:

“Wallahi ba a samu [tikitin] ba; har zuwa ranar Laraba ma an ce babu—[ni kuwa] a so na Talata da safe in kama hanya”.

Shi ma wani bawan Allah wanda ya bayyana cewa da kyar ya samu tikitin ranar Larabar, cewa ya yi makon jiya da ya je ofishin tikitin bai samu ba saboda mutane sun cika har waje.

Ga galibin mutanen wadansu jihohin arewa dai hanyar da ta bi ta Jihar Kaduna zuwa birnin na Abuja ce hanya mafi sauki.

Karin bayani