Za a bayyana sakamakon zaben Masar ranar lahadi

'Yan takarar Shugabancin Masar biyu Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Za a bayyana sakamakon zaben Shugabancin Masar ranar lahadi

Hukumar zaben Kasar Masar ta ce a gobe Lahadi ne za ta bayyana sakamakon zaben Shugaban Kasar zagaye na biyu da aka yi a makon jiya, bayan jinkirin da aka samu.

Hukumar zaben ta ce ta saurari korafe korafen 'yan takarar guda biyu ne wato Muhammad Mursi daga kungiyar 'yan uwa musulmi ta Muslim Brotherhood da kuma tsohon Firayim Ministan Kasar Ahmed Shafiq.

Dukkanin 'yan takarar guda biyu dai sun yi ikirarin samun nasara a zaben, kuma dukkaninsu sun ce za su kafa gwamnatin hadin kan kasa.

Tuni dai magoya bayan jam'iyyar 'Yan'uwa Musulmi a kasar suka ce za su ci gaba da kasancewa a dandalin Tahrir dake tsakiyar birnin duk kuwa da gargadin da Majalisar mulkin sojin kasar ta yi na cewa ba za'a bari su kawo cikas ga harkokin yau da kullum a birnin ba.

Masu zanga zangar wadanda suka iso Dandalin bayan sallar Juma'a na bukatar a bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a karshen mako ne amma aka yi jinkirin sanar da sakamakon zaben.

Wasu rahotannin da ba hukumomi ne suka bayar da su ba, sun nuna cewa dan takarar 'Yan'uwa Musulmin ne, Mohammed Morsi, ya lashe shi.

Sai dai abokin hamayyarsa, tsohon Firaminista, Ahmed Shafiq, ya musunta hakan.

Karin bayani