An yi asarar rayuka bayan kifewar kwale kwale a Kebbi

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Image caption Mutane bakwai sun mutu bayan da wani kwale kwale ya kife a Birnin Kebbi

Rahotanni daga garin Birnin Kebbi dake arewacin Najeriya na nuna cewa masu aikin ceto na can suna cigaba da laluben gawarwaki a cikin wani kogi dake daf da garin, bayan da wani kwale-kwale ya kife da wasu mutane goma sha bakwai da yammacin jiya.

Mahukuntan a garin dai sun ce ya zuwa yanzu an samu tsamo gawarwakin mutane bakwai, yayin da mutane shidda suka samu tsira da ransu, idan aka hada da matukin jirgin

Bayanai daga birnin Kebbi dai sun nuna cewar galibin wadanda suka mutu mata ne 'yan kasuwa dake kokarin tsallaka kogin domin komawa kauyen su na Bunga Sabuwa bayan tashi daga cikin kasuwa a babban birnin Jahar Kebbin

Shugaban Karamar hukumar Birnin Kebbin dai ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Wasu bayanai dai na nuna cewa kwale- kwalen ya kife ne bayan ya ci karo da wani shinge wanda wani kamfanin da ke aikin haka wata gada a saman kogin ya kafa.

Sai dai galibin mutane na ganin hadarin ya auku ne sakamakon daukar mutane fiye da kima da kwale kwalen ya yi wanda aka tsara domin ya dauki mutane goma sha bakwai.