Zanga zangar nuna kyamar tsuke bakin aljihu a Khartoum

An kone tayu a zanga zangar birnin Khartoum na Sudan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga zanga a Khartoum sun yi arangama da 'yan sanda

Masu zanga zanga a Khartoum babban birnin kasar Sudan, sun kona tayu, su ka rika jifa da duwatsu akan 'yan sandan dake kokarin kwantar da tarzomar adawa da manufofin gwamnatin kasar na tsuke bakin aljihunta.

Da farko dai dalibai ne suka fara zanga zangar, to amma rahotanni na nuna cewa, ta na yaduwa zuwa sauran al'ummun kasar.

An dai umurci 'yan sandan Sudan da su dau mataki cikin gaggawa don kawo karshen zanga zangar.

Wakilin BBC ya ce, hukumomin kasar na fargabar aukuwar gagarumar zanga zanga.

Sau biyu a cikin karnin da ya gabata ake tunbuke gwamnatin kasar sakamakon zanga zangar da ta zamanto juyin juya hali.

Karin bayani