Boko Haram ta nesanta kanta da sa bam a masallaci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Malam abubakar Shekau

A Najeriya Kungiyar Ahlul sunnah lil da'awati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram ta nesanta kanta daga wani yunkuri da wasu suka yi na tada bam a Masallacin Juma'a na Fagge a Jihar Kano.

Kungiyar na cewa mabiyanta na yin aiyuka ne na Jihadi don kafa tsarin musulunci; "ta yaya za su lalata masallaci inda ake bautar Allah?"

A ranar Juma'a ne dai aka gano wani bam da aka sa a Masallacin Juma'a na Fagge gab da lokacin da za a yi sallar Juma'a.

Kungiyar na zargin cewa makarkashiya ce jamian tsaron SSS suka yi don bata ma ta suna. Sai dai dan gane da wannan zargin kokarin samun Jami'an tsaron na SSS ya ci tura.

A wata sanarwa da Kungiyar ta futar ta hanyar sadarwa ta email wadda BBC ta samu Kungiyar ta kuma ce tayi murna da shahadar da daya daga cikin mabiyanta wato Habibu Bama ya yi wanda Jami'an tsaro suka ce sun kama shi a Damaturu, babban birnin Jihar Yobe.

Karin bayani