Girka na bukatar sake yarjejeniyar bashi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Girka

Kasar Girka tana bukatar a sake yarjejeniyar bata bashin ceto ta daga matsalar tattalin arziki da ta zo mata iya wuya.

Girkar ta na son ta dage yarjejeniyar rage albashi da haraji ne ta kuma dakatar da batun rage ma'aikata sannan kuma ta kara yawan tallafin da ta ke baiwa marasa aikin yi.

Athens din ta na kuma bukatar karin lokacin da zata rage gibin kasafin kudinta..

Wakilin BBC ya ce sassaucin da Girkan ta ke fatan samu a yanzu ya fito karara kuma ya zarta yadda ake tsammani da farko.

Haka kuma ana ganin cewa kasar Girkar ba za ta iya cigaba ba; ba tare da samun tallafin kasashen turan ba.

Karin bayani