An tusa keyar El Baghdadi El Mahmoudi zuwa Libya

Libya Hakkin mallakar hoto NA
Image caption Ana zargin Al Mahmoudi da hannu a miyagun laifukan da gwamnatin Marigayi Gaddafi ta aikata

Hukumomin kasar Tunisia sun tisa keyar tsohon Firayim Ministan kasar Libya El-Baghdadi Al-Mahmoudi, zuwa kasar sa ta Libya.

Mr. Al-Mahmoudi ya yi aiki a karkashin mulkin tsohon shugaban Libya Mu'ammur Gaddafi a matsayin Firayim Minista na tsawon shekaru biyar kafin ya tsere zuwa kasar Tunisia a watan Agustan bara, lokacin da 'yan tawayen kasar Libya suka kwace babban birnin kasar Tripoli.

Ana danganta El-Baghdadi Al-Mahmoudi, a Libya da hannu a miyagun laifukan da gwamnatin Mu'ammar Gaddafi ta aikata, a lokacin da take kokarin murkushe juyin juya halin da ya yi sanadiyyar tumbuke gwamnatinsa da kuma halaka shi.

Karin bayani