Harin da aka kai gidan yari a Yobe ya yi sanadiyyar mutuwar fursuna daya

Goodluck Jonathan
Image caption Fursuna daya ya mutu bayan 'yan bindiga sun kai hari gida yari a Yobe

Hukumomin tsaro a jahar yobe dake arewacin Najeriya sun ce an kashe fursuna daya tare da raunata wani dogarin gidan yari bayan wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai wa babban gidan yari garin Damaturu babban birnin jahar da safiyar yau

Wani mazaunin garin na Damaturu ya shaida wa BBC cewa sun kwashe kimanin mintuna 30 suna jin karar harbe-harbe da tashin bama-bamai daga inda gidan yarin yake.

Kwamishinan 'yan sandan jahar Yobe Mr. Patrick Egbuniwe ya tabbatar da afkuwar harin.

Ya kuma ce jami'an tsaro sun hallaka wani adadin da ba'a tantance ba daga cikin maharan.

Sauran maharan dai sun samu damar kwashe gawawwakin 'yan uwansu, kana su ka gudu dasu.

Karin bayani