Sabon Shugaban Masar ya fara aiki

Mohammed Mursi Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Sabon shugaban kasar Masar, Mohammed Mursi, ya fara aiki a karo na farko inda ya ke kokarin kafa sabuwar gwamnati.

Mohammed Mursi ya shiga Ofishin da a da tsohon Shugaban kasar Masar, Hosni Mubarak ya zauna.

Wani na hannun damar sabon shugaban ya ce tuni Mr Mursi ya soma tattaunawa tare da tuntubar jama'a game da kafa sabuwar gwamnati.

A jiya dai sabon shugaban ya bukaci hadin kan jama'ar kasa, inda ya kara da cewar juyin juya halin da ya kawar da tsohon Shugaba Mubarak zai ci gaba har sai ya cimma burinsa.

Karin bayani