'An yi kuskure da aka kori El-Baghdadi daga Tunisia'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Moncef Marzouki

Shugaban kasar Tunisia ya ce matakin gwamnatinsa na korar tsohon Firayim ministan Libya, El-Baghdadi El-Mahmoudi, zuwa gida ya sabawa doka.

Shugaba Moncef Marzouki ya ce Firayim ministansa Hamadi Jebali bai shawarce shi ba kafin daukar matakin.

Al-Mahmoudi dai ya rike mukamin Firayim minista a gwamnatin hambararren shugaban kasar Libya, Kanar Mo'ammar Gaddafi, tsawon shekaru biyar kafin ya yi kaura zuwa Tunisia a watan Agustan bara.

Masu kare hakkin dan Adam sun ce akwai yiwuwar kashe shi za a yi a Libya amma gwamnatin Libyan ta ce za a tabbatar ma sa da hakkokinsa.

Karin bayani