Mursi ya yi alkawarin gudanar da mulki nagari a Masar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mursi na jagorantar Sallah don nuna farin cikinsa ga Allah

Dubban Misrawa ne suka kwana suna shagulgula a dandalin Tahrir bayan da hukumar zaben Masar ta bayyana Muhammad Mursi a matsayin zababben shugaban kasar na farko.

A jawabinsa, Muhammad Mursi na kungiyar 'yan uwa Musulmi, ya dauki alkawarin gudanar da mulkinsa ba tare da nuna wariya ga kowanne dan kasar ba.

Da alama ya yi wannan kalami ne da zummar farantawa mata da kiristoci kifdawa, wadanda ke ganin ba za a yi musu adalci ba rai.

Mista Mursi ya godewa ubangiji sannan ya yabawa sadaukarwar Misrawa bisa samun nasararsa.

Za a yi wa kowa adalci

Jawabin nasa, wanda aka watsa ta gidan talabijin na kasar, sabon shugaban kasar, ya ce gwagwarmayar da Misrawa suka kwashe fiye da shekara guda suna yi don kawar da mulkin zaluncin da hambararren shugaba Hosni Mubarak ke yi da kuma tabbatar da mulkin adalci ta biya.

A cewarsa, abin da zai fi bai wa muhimmanci shi ne gina sabuwar Masar mai yalwar tattalin arziki.

Ya ce: "A shirye nake na hada kai da ku domin gina sabuwar Masar mai bin tsarin dimokaradiyya na zamani. Zan shafe kwanakin da nake aiki wajen tabbatar da hakan, amma fa ta hanyar yin la'akari da tsari da kuma asalin mu .Zan hada kai da ku don kare tsaron kasar Masar a kasashen Larabawa, da Afirka, da ma duniya baki daya.Muna mikawa duniya sakon zaman lafiya.Haka kuma za mu cigaba da aiwatar da yarjejeniyar da Masar ta sanyawa hannu da kasashen duniya''.

A dandalin Tahrir kuwa, inda can ne cibiyar gangamin samun sauyi, jama'a ne ke cigaba da murna saboda ayyana Mista Mursi a matsayin sabon shugaban kasar, suna masu cewa cike suke da fata na samun sauyi a kasar.

Kasashen duniya sun taya Masar murna

Kasashen duniya ma sun bayyana jin dadinsu game da sauyin siyasar da aka samu a Masar inda shugaban Amurka, Barack Obama, ya kirawo Mohammed Mursi ta wayar tarho yana mai taya shi murna ta zama zababben shugaban kasa na farko a Masar.

Ya ce a shirye Amurka take ta marawa kasar baya a yunkurinta na girka dawwamammen mulkin dimokaradiyya.

A zirin Gaza ma, inda jam'iyar Hamas ke kawance da ta 'yan uwa Musulmi, dubban Palasdinawa ne suka hau kan tituna don bayyana farin cikinsu.

Pirayim Ministan Gaza, Ismail Haniyeh, ya taya Misrawa da sabon shugabansu murna:

Ya ce: "A madadin Palasdinawa da kuma gwamnati, muna taya Misrawa murna saboda sauyin da suka samu na mulkin dimokaradiyya sakamakon abubuwan da suka wakana a dandalin Tahrir da kuma rumfunan zabe.Ina taya Dr. Mohammed Morsi murnan lashe wannan zabe''.

Karin bayani