Jam'iyyar ANC mai mulkin Afirka na taron shata manufa

Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sauran watannin 2012 za su zowa Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu da zafi

A wannan makon ne jam'iyyar ANC mai mulki a Afrika ta Kudu ke taron shata manufarta a birnin Johannesburg.

Taron, wanda ake yi sau daya a cikin shekaru biyar, na da aniyar tattaunawa a kan alkiblar da jam'iyyar—wadda ke kan mulki tun 1994—za ta dauka a gaba.

To amma yayinda rashin aikin yi ke karuwa da kusan kashi ashirin da biyar cikin dari, ga alama taron fi mayar da hankali ne makomar Shugaban kasar Jacob Zuma.

Akwai dai yiwuwar watannin da suka saura a shekarar 2012 za su kara zafi ga Shugaba Zuma, kuma taron na kwanaki uku wanda aka fara ranar Talata ma'auni ne na irin dumin yanayin da zai fuskanta.

A watan Disamba Mista Zuma zai fuskanci zaben da za a gudanar lokacin babban taron jam'iyyar, shekaru biyar bayan tube wanda ya gabace shi a kan kujerar shugabancin jam'iyyar, Thabo Mbeki—manufar taron na wannan makon dai ita ce shiryawa babban taron jam'iyyar.

Babbar matsalar da Mista Zuma ke fuskanta ita ce: ana kara juya masa baya a jam'iyyar, kasancewar tsofaffin abokan huldarsa kamar kungiyoyin kwadago sun yi hannun riga da shi saboda gazarawarsa wajen samar da ayyukan yi.

Haka zalika, tun bayan hawansa kujerar shugabancin kasar a shekarar 2009, ya sha fama da abin kunya wanda har ya shafi iyalinsa.

Saboda haka ne ma wadansu daga cikin kusoshin ANC din suka fara tunanin ya zamewa jam'iyyar kaya.

Mai yiwuwa wadannan masu sukar lamirin Mista Zuma su yi amfani da wannan taro don kafa turakun taka birki ga yunkurinsa na sake hayewa kujerar shugabancin jam'iyyar da ma na kasar.

Daga cikin batutuwan da za a tattauna wadanda za su iya kawo rarrabuwar kawuna har da batun mayar da bangaren hakar ma'adinai na kasar hannun 'yan kasa, wanda jagoran matasan jam'iyyar da aka kora, Julius Malema, ya yi ta fafutukar ganin an yi.

Zai yi wuya jam'iyyar ta amince da wannan mataki yayin wannan taro, amma kuma mai yiwuwa wadanda ke adawa da Mista Zuma su yi amfani da wannan damar don kara nesanta kansu da shi.

Wani batun kuma shi ne na kundin da ake kira “Sauyi na biyu”, wanda ke nuni da cewa tun bayan hawan ANC mulki shekaru goma sha takwas da suka wuce ta fi mayar da hankali ne wajen tabbatar da dimokuradiyya a kasar; don haka sauyin da za ta samar na biyu shi ne inganta tattalin arziki da samar da ayyukan yi.

Mista Zuma dai na goyon bayan irin wannan tunani, amma kungiyoyin kwadagon da ke da alaka da jam'iyyar sun yi fatali da kundin.

A cewarsu, kamata ya yi tun tashin farko jam'iyyar ta fara samar da ayyukan yi.

Ga alama shi ma mataimakin shugaban kasar, Kgalema Mothlanthe, wanda kuma shi ne barazana mafi girma ga Mista Zuma, bai amince da kundin ba.

Watakila ma shi ya sa yayin jawabinsa na bude taron, Mista Zuma ya jadddada cewa har yanzu ragamar tattalin arzikin kasar na hannun tsiraru fararen fata.

Sai dai kuma takaddama a kan gazawar shugaban ta cimma wani abin-a-zo-a-gani a wannan bangaren ka iya haddasa rikicin da zai fito da tataburzar karbe ragamar shugabancin jam'iyyar bainar jama'a.

Karin bayani