'Yan Burtaniyar da ke karbar horon ta'addanci na karuwa'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jonathan Evans

Shugaban Hukumar Leken Asirin Burtaniya, MI5 ya ce ana samun karuwar 'yan kasar da ke zuwa kasashen Larabawa domin samun horo a kan ta'addanci.

Jonathan Evans ya ce ana hasashen cewa kimanin mazauna Burtaniya dari biyu ne ke da alaka da kungiyoyin 'yan ta-da-kayar-baya a kasashen Larabawa, inda al-Qaeda ke kara samun matsuguni tun farkon juyin-juya-hali a yankin.

A cewarsa, 'yan tayar da kayar-bayan da aka haifa a Burtaniya na karbar horon ta'addanci a kasashe kamar Libya da Masar kuma akwai yiwuwar su dawo Burtaniya don kaddamar da hare-hare.

Ya ce hakan wani abin nuna damuwa ne.

Mista Evans ya ce yanzu haka jami'an tsaron Burtaniya sun mayar da hankalinsu ne a kan wasannin Olympics da za a fara a watan gobe a London domin kawar da yiwuwar fuskantar ta'addanci.