Mutane 70 sun bace a zaftarewar kasa a Uganda

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Uganda

Kungiyar bada agaji ta Red Cross a Uganda ta shaidawa BBC cewar kusan mutane 70 sun bace, sakamakon zaftarewar kasa inda gidaje suka nitse a kusada tsaunin Elgon a jiya Litinin.

A yanzu haka dai an tabbatar da rasuwar mutane 18. Wadanda kuma suka rasa 'yan uwansu, sun rika kuka a inda lamarin ya auku.

Ministan agajin gaggawa na Uganda, Steven Malinga ya ce abinda gwamnati zata maida hankali akai shine kwashe mutanen da suka tsira da ransu daga yankin, amma kuma wasu mutanen sun ki yarda a daukesu daga cikin gidajensu.

Ministan ya kuma kara da cewa matsawar aka kara ruwa mai karfi sosai kusan mutane dubu dari hudu ne zasu iya rasa gidajensu a tsaunin Mount Elgon.

Karin bayani