Jami'an tsaro a Najeriya sun yi kira ga kara tsaro a wuraren ibada

Image caption hare hare a Najeriya

Hukumar 'yan sanda a Najeriya, ta yi kira ga masu kula da wuraren ibada na Musulmi da Kirista, da su kara tsaurara matakan tsaro a masallatai da coci-coci domin rage yiwuwar kai musu hare-hare.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wasu shawarwari da ta fitar a yau ga masallatai da kuma coci-coci domin kare kansu daga hare-haren da ta kira na ta'addanci da ake kaiwa wuraren ibada a kwanakin nan.

Sai dai hukumar ta ce shawarwarin, ba wai suna nuna cewa 'yan sanda sun gaza ne wajen kare lafiya da dukiyoyin jama'a ba.

A 'yan kwanakin nan dai an kai hare hare da dama a wuraren ibada na mujami'o'i a garuruwa daban daban, an kuma yunkuri sa wani bam a masallacin Juma'a a Jihar Kano.

Karin bayani