Arsenal za ta kara da Super Eagles

'Yan kwallon Arsenal
Image caption 'Yan kwallon Arsenal

Arsenal za ta je Najeriya domin yin wasan sada zumunta da 'yan wasan Najeriyar Super Eagles a Abuja ranar 5 ga watan Agusta na wannan shekara.

Najeriya wadda take ta 60 a jerin kasashe na hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA, za ta kara da Arsenal din ce wadda ita kuma ta zo ta uku a gasar Premier Ingila da ta gabata.

Wannan dai shi ne karon farko da Arsenal din za ta yi wasa a Najeriya.

Jami'in kamfanin da ya hada wasan Danjan Sports, Mai suna David Omigie ya ce ''hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Najeriya ta amince za ta sanya zaratan 'yan wasan Najeriya a karawar.

Kuma shi ma kocin Arsenal zai yi amfani da wannan dama ya jarraba cikakkun 'yan wasan da zai yi amfani da su a kakar wasannin da za a shiga.''

A shafinsu na Internet, jami'an Arsenal din sun ce kulob din ya ziyarci Afrika ne tun a watan Yuli na 1993 yayin rangadinsa a Afrika ta kudu, kuma zai sake dawo wa Afrikan ne a wannan karon saboda gagarumin goyon bayan da suke samu ba kawai a Najeriya ba, a Afrikan baki daya.

Karin bayani