Ana binciken cuwa-cuwa a manyan bankunan duniya

Kudin euro Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Ana zargin bankuna da cuwa-cuwa

Masu sa ido a kan harkokin bankuna a Amurka da kasashen Turai da nahiyar Asiya suna gudanar da bincike a kan zargin da ake yi cewa wadansu daga cikin manya-manyan cibiyoyin hadahadar kudade suna yin cuwa-cuwar da ta ke shafar abin da miliyoyin masu karbar bashi ke biya.

Ranar Laraba aka yiwa bankin Barclays tara ta dala miliyan dari hudu da hamsin.

Mai yiwuwa tarar da aka yiwa bankin na Barclays, wadda kawo yanzu ta zarta kowacce tara girma, ta kasance tamkar cikin cokali.

Domin kuwa a yanzu haka ana gudanar da bincike a kan bankuna fiye da ashirin a kasahse daban-daban dangane da irin wannan cuwa-cuwa.

Ana jin wannan bincike ya shafi bankunan Citigroup da JP Morgan da Deutsche Bank da HSBC da Royal Bank of Scotland da kuma Lloyds Bank.

Zargin da ake yiwa wadannan bankuna shi ne sun yi muna-muna a kan kudaden ruwan da aka biya a kan basussukan da bankuna ke baiwa junansu a tsakanin shekara ta 2005 da shekara ta 2009.

Bankunan su kan yi hakan ne kuwa ta hanyar shara karya a kan adadin abin da ya kamata su biya idan bashi ya shiga tsakaninsu.

Karin bayani