Darajar hannun jarin bankuna ta fadi kasa warwas

shares Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Babu tago mashi a harkar hannun jari a duniya

Darajar hannayen jarin bankuna sun fadi kasa, bayan da masu lura da harkokin bankuna a Amurka, kasashen Turai da Asia suka gudanar da bincike kan bankunan da ake zargi da cuwa-cuwa kan wasu kudade.

A birnin London hannayen jari a bankin Barclays, ya yi kasa da kusan sama da kashi 15 bisa dari.

Yayinda Bankin Scotland yayi asarar fiye da kashi 11 bisa dari.

A birnin Newyork kuwa bankin JP Morgan ya fadi ne da fiye da kashi 4 bisa dari.

Ministan harkokin kudin Birtaniya, George Osborne ya ce binciken ya nuna cikakkiyar gazawa a fannin tsarin harkokin kudade.

Karin bayani