Tarayyar Turai ta amince da tallafawa bankuna

shugabannin tarayyar turai Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption shugabannin tarayyar turai

Shugabannin kasashen Tarayyar Turai sun amince da sababbin matakan farfado da tattalin arziki.

Manufar bullo da matakan ita ce raba alakar da ke tsakanin bankuna masu rauni da gwamnatoci da kuma taimakawa kasashen da ke fama da dimbin basussuka.

An amince da matakan ne a babban taron da shugabannin suka yi a Brussels, inda suka amince da sayen basussuka da takardun lamunin gwamnatocin kasashen yankin.

Wadannan matakai na cikin abubuwan da kasashen Spaniya da Italiya suka nema don takaita basussukan da suke karba.

Karin bayani