Ansaruddin ta umarci Abzinawa 'yan tawaye su bar Timbuktu

Mayakan Ansaruddin a arewacin Mali Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mayakan Ansaruddin a arewacin Mali

Dakarun kungiyar Ansarud Deen masu tsattauran ra'ayin addinin Islama a arewacin Mali, wadanda suka karbe garin Gao daga hannun ’yan tawayen Abzinawa, sun umarci ’yan tawayen su fice daga birnin Timbuktu.

Sai dai har yanzu babu wani martani daga bangaren Abzinawan.

Mazauna garin na Gao sun ce garin ya yi tsit bayan gumurzun da ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane ashirin.

Abzinawan dai sun ce daya daga cikin shugabanninsu Bilal Acherif ya samu rauni a yayin fadan, kuma an garzaya da shi Burkina Faso domin a yi masa magani.

Wani mazaunin garin na Gao, Shekarau na Alhaji Sambo Gao, ya shaidawa BBC cewa da safiyar ranar Laraba an yi ta jin karar harbe-harbe a wajen garin.

“Mu mutanen gari muna nan lafiya kalau, babau wanda ya taba mu”, in ji Malam Shekarau, wanda ya kara da cewa tuni mutane sun ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.